Hausa Novels Complete Documents

Dare Daya Hausa Novel Page 35-36

Sponsored links

aeduk ƙauyen nan ina ji babu wacce takaita cika ga uwa uba kin bari tayi karatun boko da ake cewa idan mace tayi sa lalacewa take amma naga Hafsat yarinya mai hankali Dan Asabe yana ta yabonta babu ruwan ta ko magana bata son yi, INNA taji mugun daɗi har cikin ranta tana cewa kenan haka mutanen ƙauyen nan ke dauka na barta ne tayi karatu dan ta daukaka babusan dan ta lalace na barta tayi karatun boko bah washe baki tayi tace bara naje karna makara, ta tashi tana karkaɗe tsumokaran zanen ta Attika ta raka har soro kafin ta dawo Dan Asabe sai washe baki yake yana tunanin yacce zai yiwa Hafsat cin kaca sai ya cacccaki durinta son ransa sai yayi sati baya fita sai murmushi yake haka Attika tazo ta same ta itama ta ta yasa farin ciki nan ya shiga neman masu aeki domin a gyara masa wani Ɗaki a kuma shafa masa pain yayi kyau. INNA na fitowa gidan su dan Asabe ta tafi tasha, Tashiga motar gusau daga sai karfe uku na rana ta isa gusau daga nan ta shiga mota zuwa ƙwatar ƙwashi sbd hanya bakyau sai 4 ta isa bazan faɗi sunan ƙauyen bah gaskiya nan ta shiga wani dan ƙaramin ƙauye wanda mutanen cikin sa yan tsiraru Sam basuda yawa domin gaba daya bazan su da matan su ba zasu wuce su 100 ba sai hada hadarsu suke haka ta ratsa mutanen ƙauyen ta hau wani tsauni dutse ne mai tsayi sosai ga faɗi gaba ɗaya shiya canye rabin ƙauyen domin yana faɗi sosai haka ta ringa tafiya akan dutse saida tayi tafiyar da ta cita mintuna sama da 20 kafin ta kai ga wani ƙogo inada dutse ya buɗe kamar ƙofa anyiwa hanyar pain da jini da wani farin pain sai gefe gefen ƙofar a saka wani dogon icce sai ƙwaranƙwal din kan mutun guda biyu akai, ajiyar zuciya ta sauke ta jiuya dama da hagu dinta ta ɗaga hannu sama da maido ƙasa har sau uku ko wane gefe kafin ta jiuya ta shiga ƙofar da baibai(da baya da baya) saida ta kai tsakiyar dakin kafin ta jiuyo tana sarkin almatsu baka haifa bah kuma ba’a haife kaba innalillahi wa’inna ilaihi raji’un Allah ubangiji ya rabamu da shirka Allah ubangiji ya rabamu da ƙwaɗayin abun duniya Allah ya rabamu da son zuciya Allah kasa muna tsoronsa ako da yaushe Allah kasa mufi ƙarfin zuciyoyin mu kar zuciyoyin mu sufi karfin mu Ameen. Haka ta ringa yimasa kirari kala kala wasuma nan take ta fita a musulunci aka kira su nan ta ATTIKA saida duka kogon ya amsa amon sautin muryarsa……..

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button