Daudar Gora Book 2 Page 12
Wannan hali da Jasrah ta tsinci kanta a ciki ya ɗauke hankalin Malikat Bushirat da ga sanin halin da ake ciki akan komawar Iffah sashen Tajwar Eshaan ɗin. Dan kamar wasa jini ya ɓalle mata har sai da cikin jikinta da sukai matuƙar ƙwallafawa rai ita da mijinta (Miran Arshaan) gaba ɗaya ya fita har itama ana neman rasata dan itama hadima Banou ɗin taso taɓata ALLAH dai ya sa tana da sauran kwana a gaba tasha da ƙyar sai dai a ranar kam a asibitin cikin masarautar ta kwana.
Rasa cikin nan ya matuƙar ƙona ran Miran Arshaan da ita kanta Jasrahn da sai a washe gari ta dawo hankalinta har take faɗa musu dalilin shigarta wannan hali saboda likita tace musu ɓacin ran da take ciki ne ya janyo ɓarin. Sabuwar tsanar Iffah ce ta baibayesu tare da ɗaukar alwashin a sashen Shahan-shan ɗin da su malikat Haseenat ɗin suka kaita sai sun bita sun halakar da ita. Ita kanta malikat Haseenat ɗin sun ƙullaceta matuƙa dan a ganinsu ita ce sanadin komai. (basu san ita bama tasan anai ba😏).
Bayan lafawar halin da Jasrah k ciki ba ƙaramin ɓacin rai Malikat Bushirat ta nuna ba akan jin an maida Iffah sashen Tajwar Eshaan bisa wai umarninsa, sai dai sam bata yarda ba acewarta Malikat Haseenat da Daneen Ammarah ne suka saka shi yin hakan. A wannan gaɓar dai kai tsaye kowa ya fahimci fushin nata gaba ɗaya ya dangana ne ga Malikat Haseenat. Dan a take ta saka a rufe mata likitocin da suke duba Iffah, acewarta sai sun faɗa mata wanda ya sakasu yin shirin. Iya gaskiyarsu sun rantse mata akan su babu ruwansu umarni kawai aka basu. abinda kuma ya samu Iffah gaskiya ne kuma bincikensu ne ya basu da iliminsu. Bata nuna alamun zata saurarensu ba ma balle yarda da abinda suke faɗa ɗin, sai ma sabon bincike data saka akan zaman Iffah kurkuku. Sai dai me hatta jami’an da Malikat Haseenat tasa suke tsaron Iffah sunƙi faɗar kowane sirri, hakan sai ya sake hargitsa mata lissafi ga kuma su Miran Arshaan na tunzurata a gefe da sake munana tsohuwa Malikat Haseenat da komai dake faruwa tana ji amma ko tari taƙiyi balle ta nuna tama san da abinda Malikat Bushirat ɗin keyi. Ta dai aika Yumma (ƙanwarta da take tare da ita) taje ta duba Jasrah a randa tai ɓari…
A hankali ya janye idanunsa da ga kallon inda taken cike da basarwa yana amsa sallamar Doctor Afif da ya shigo ɗakin akan lips. Dr Afif ya ƙaraso cikin ɗakin yana mai rissinawa ya gaishesa, da idanu ya amsa masa kawai alamar ƴan izzar na kusa. Shima Dr Afif ɗin bai damu ba, dan a ɗan zaman jiyyar nan har ya fara haddace magana da idon nan. Gaban gadon ya ƙarasa yana sake rissinawa a cikin girmamawa ya miƙa masa file ɗin hannunsa.
“Wannan shine file ɗin dukkanin bayanan nata da likitocin suka tattara. Sai dai suna kan sake bincike akan rashin farfaɗowar tata kan lokaci da ya kamata ace tayi tun kwanaki biyu da suka wuce”.
File ɗin ya amsa batare da yace komai ba, ya ɗan dudduba, sai kuma ya ɗago idanunsa ya sake zubasu kan Dr Afif ɗin. Sai da yaja wasu sakanni kafin ya iya furta abinda ke bakinsa da ƙyar. “Kai mi ka fahimta akan hakan?”.
Tsaiwa Dr Afif ya gyara yana mai sake rissinar da kansa. “ALLAH ya ƙara maka lafiya da tsohon rai mai albarka ni ina ganin ko za’a sake neman wani ƙwararren likitanne akan al’amurin nata da ya fi waɗan nan ɗin ƙwarewa. A yanda suka san aikinsu bai kamata ma ace sun gagara gano wani ƙwaƙwƙwaran abu guda ɗaya ba har zuwa yanzun, dan dole akwai abinda akai mata, dan bazai yiwu ace ta kasance a wannan halin babu ƙwaƙwƙwaran dalili ba”.
Ɗan murmushi Tajwar Eshaan ya saki a karo na farko, batare da ya cema doctor komai akan bayaninsa ba ya ziro fararen ƙafafunsa zuwa ƙasa. Slippers ɗin dake ajiye gaban gadon ya saka, murya a dake ya furta, “Zan ganta”. Da sauri Dr Afif yay gaba yana faɗin, “Bismillah ranka ya daɗe”.