Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 44

Sponsored links

Sameer daya zama speechless ya kurawa khaleel ido batareda yace komai ba…….

Tuki suke da dan sauri motar mami na tsakiyar ta police dake biye dasu kasancewar Deen motarta aka barshi ya shiga saboda matsayinta na ‘Chief Justice’…….

Driving mami take cike da damuwar abinda Deen ya dauko musu, Allah yasani Deen is her beautiful distraction, of course beautiful tinda hannunka baze rube ka dauka ka yarba…..

Shiko gogon hankalinsa kwance kamar ba station suka nufa ba,shi damuwarsa daya yanda ya tafi ya barta batareda ta farka ya tambayeta ‘WACECE ITA’ ba, gashi yanzu duk ta hargitsa masa lissafi,daya rufe ido ita kawai yake gani da beautiful face dinta that is treacherous,sai yaji dama bai kalleta ba da kila yana cikin peace yanzu…..

“Nace what crime have you committed again?”…….

Ya jiyo muryar mami na fadin haka,sai a lokacin ya dawo daga duniyar tinanin daya lula…..

Cikin rashin sanin abinda zai fada yace….

“Bangane ba mami?”……

Hade fuska tayi sosai tace…..

“Zaka gane idan ka tsinceka a cikin cell suna jibgarka”……

“Tabdi jam! Wa zaa jibga? Ni? Allah ya kiyaye, wallahi sai na zubarwa duk wanda yayi gigin tabani hakora!”……..

“You see your issue ko? Stubbornness! Bansan a ina ka kwaso wannan mugun halin ba! Well baze wuce ubanka ba!”…….

Shafa gemunsa yayi yana smirking yace….

“Kunfi kusa(haka yake fada duk sanda kowannensu ya zagi daya a gabansa danshi ya kasa gane meya hadasu da suke rashin jituwa haka), but seriously mami banyi komai ba, I don’t know even know what they’re accusing me of”..

“What ever it is zamuji in munje, Idan kuma kasa naji abinda yasa zuciyata ta buga na fadi na mutu, sai ka zuba ruwa a kasa kasha tinda haka kakeso dama!”….

 

Wani iri Deen yaji a ransa musamman datace haka kakeso dama sai yaji wani guilty feeling ya kamasa,marairaicewa yayi kamar wanda ake forcing dinsa yayi magana yace….

“I’m sorry”…..

Bata kulashi ba duk da irin mamakin data shiga akan hakurin daya bata dan tasha masa fada yayi tafiyarsa ya barta a gurin ko a jikinsa……

Shigowarsu station din yayi daidai da shigowar Dad da securities dinsa….

Kallon mami Dad yayi yana mamakin ya akayi tazo? Kodai Deen yana gurinta a abuja dama,tabbas biri yayi kama da mutum inba hakaba meya hada Deen da zaman abuja, wato itace ta janyeshi duk neman da yake masa da tsare likitocin da basuji ba basu ganiba na watanni akan sai yaga danshi ze sakesu, ashe dan yana gurin uwarsa…. A take zuciyarsa ta hau ta zauna akan lallai Deen yana gurinta duk wannan neman dayake masa……

Yan sandan basu bawa kowa damar magana ba suka fara bayanin abinda ya faru…..

 

“He’s accused of criminal robbery , sannan ya kashe mutune uku mun kuma tabbatar da haka ne ta dalilin thumbprint dinsa dake kan gun din dayayi kisan, minutes before he had an accident”….

 

“What?!! This must be a joke!”

 

Mami ta fada a zafaffe …..

 

Taran numfashinta dad yayi kamar wanda yake jira tayi magana yana fadin…..

 

“Dole kice joke mana! Duk abinda yakeyi bake kika janyo ba? Yanzu ga abinda ya dauko nan ai saiki san yanda zakiyi dashi!”…..

 

“Oh haka ma zakace? Ni banyi complain ba sai heartless person like you? Of course zansan yadda zanyi dashi because I’m not nonchalant like you!!”…..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button