Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 119

Sponsored links

“Tabbas hakane” Miran Arshaan ya amshe zancen. Batare daya jira cewar Iffah ba ya cigaba da faɗin, “Idan baki manta ba bayan kin basa shayi ya koma gefene yana kallo cikin masarauta, nima kina bani kuma na koma kusa da shi ina mai yabama tarbiyyarki da tabbatar masa yayi dace mace tagari data dace da shi a yanzu. Buɗar bakinsa sai ya sake tsaki da faɗin, “Tukunna dai, ai shi har yanzu matar da zai rayu da ita bata iso ba. Naji mamaki harna tambayesa ba’asin hakan amma sai bai tankani ba kin sanshi da girman kai. Zancen ya tsaya min a rai nazo na sami Jasim Akh da maganar, shine fa ya duƙufa bincike harya samu ganawa da kakanki da ke a ƙauyen Jumna”.

 

Sosai Iffah ta zabura da jin sun gana da kaka harta ɗago ido ta na kallonsu. Tabbas sihiri gaskiya ne, kuma yakanci kowama tunda har yaci ma’aikin ALLAH. A take wani abu mai sanyi ya dinga shiga jikin Iffah tamkar ana kwararashi cikin jininta. Hawaye ne suka silalo a idonta ta buɗe baki a hankali ta furta “Tabbas zan kashesa da hannuna, zan kashesa da dafin maciji na gaskiya kamar yanda yake halaka mutane dana tsafi. Nayi alkawarin yanda ya wargaza min ahali nima sai na wargaza rayuwarsa..”

 

 

Miran Arshaan da Miran Jasim suka kalli juna sukai murmushi. “Zako mu baki dukkan gudunmawar da kike buƙata Ibnati. Tare da kariya ta musamman ga duk wanda zai iya kawo miki hari, balle ma a yanzu abinda zakiyi sai dai ya ƙara kawo miki ɗaukaka dan irinki ƙasar ruman ke nema. Mi kike buƙata a yanzu?”.

Kai tsaye ta amsa da cewar, “Dafin maciji mai matuƙar haɗari”.

“Zako ki sami na macizai ma ba maciji kawai ba. Ki saurari saƙo zuwa safiyar gobe. Mun barki lafiya”.

Wani irin kuka mai taɓa zuciya Iffah ta saki, a hankali ta zame takai kwance kanta da yay mata nauyi na sara mata. Gaba ɗaya duniyar tai mata dummm bata gane komai, burinta kawai shine ta ɓatar da Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed. Gawarsa kawai tafi bukatar gani kwance a ƙasa fiye da komai. So take taga ahalinsa na kuka fiye da wanda sukai a dalilin rasa ƴan uwansu saboda son kansa. Haka ta kwana a wani irin bahagon yanayin da bazata iya koda tunawa ba. Ita bamai barci ba ita ba ido biyu ba, ita ba matacciya ba ita ba mai rai ba gadai tanan. Duk da tana fashin salla ana kiran salla ta miƙe, bayi ta shiga ta tsaftace jikinta duk da babu wani ƙazanta tattare da ita, tana ƙoƙarin naɗe gashinta daya ɗan warware takeji kamar magana a ƙofar ɗakin nata. Cikin shakku ta gyara rigar wankar jikinta ta nufi ƙofa ta buɗe. Da mamaki take kallon amintacciyar hadimarta mai suna Abal dake a durƙushe hanunta ɗauke da ƙyakywan bowl.

 

Da sauri Abal takai ƙasa tana gaidata. Batare da Iffah ta amsa ba ta ɗaga bakinta da yay mata nauyi da ƙyar tace, “Lafiya…..?”

 

“Lafiya Lau ya Zawjata-almilk. Saƙone daga sashen mai Babban ɗaki”.

 

Hakan ya ɗan saka Iffah a shakku da mamaki, amma sai bakinta yay mata nauyi bata iya ta sake cewa komai ba ta amshi tambulan ɗin mai ɗauke da sabuwar madara fara ƙal. Idanu Iffah ta tsurama madarar wani shawa’ar shanta na fusgarta. Amma sai ta dake ta ajiye ta da nufin sai ta gama kimtsawa tasha ko kaɗanne kaffin ta sake komawa barci. Harta nufi kayan data fiddo zata saka kira ya shigo wayarta. Ruɗewa tai dan abune da bai taɓa faruwa da ita ba, kofa sallar asubahi ba ayi ba. Kamar wadda ake ingizawa da remote ta ɗauka wayar, ganin Miran Jasim ta amsa da tsumar jiki tana gaisheshi kai kace yana a gabanta ne. Bai amsata ba, sai ma umarni daya bata cikin kakkausar murya saɓanin wadda yake mata magana da ita a baya.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button