Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 92

Sponsored links

Shigar ƙamshin turarensa da bayan shi babu wani mai irinsa da sautin takun takalman ƙafarta ya sashi juya sharɓeɓen takobin dake a hanunsa cike da gwanancewa ya karci ƙasa ya gocema Aamin nasa da suke wasan tare ya juyashi zuwa hannunsa na haggu saɓanin na dama sai gashi akan wuyan Iffah da numfashinta yay wata irin mummunan fisga.

“Who are yo…..?”.

Yay yunƙurin faɗa cikin alamun bayyanar fushi mai haɗi da isa da ƙasaita, sai dai kalmar ta gagara ƙarasa fita a harshen nasa dalilin tozali da abinda bashi yay tsammanin gani ba. Tar-tar fuskokinsu suka bayyana akan takobin mai matuƙar ƙyalli da sheƙi da kai tsaye za’a iya kiranta faɗama jini na wuce…..

Tsam Iffah ta ƙara damƙe trayn hanunta jin rawar jikinta na neman fitowa, “Barka da safiya ranka ya daɗe”. Ta faɗa cikin ƙarfin hali da jarumtar saka idanunta cikin tsakkiyar nasa da ke tsaye a kanta har yanzu ƙyam. Sai dai duk ƙwaƙwƙwafin

mutum bazai iya gane abinda ke a cikinsu ba balle akan fuskarsa mai cike da gizago akoda yaushe. Ganin bai amsa ba, bai kuma daina kallon tsakkiyar idanunta da ayanzu take ƙoƙarin janyewa a nasa ba, bai kuma janye takobin da kallonta kawai zai iya tada tsigar jikin mutum daga wuyanta ba ya sata ɗan shammatarsa ta goce makoshinta da ga tsinin takobin daya ɗaura matan, sai dai a yanda ya wani lumshe idanu da sauke takobin yasata tabbatar da ya bartane kawai. Gaba tai yunƙurin yi, da yima hadiman da suka iso wajen yanzu nan kallon gefen ido a kaikaice ta saki wani lallausan murmushi mai ma’anoni da yawa a zahiri. A kuma ƙasan ranta ko ɗar babu.

Duk wannan abun Miran Arshaan fa na tsaye a wajen ne yana ƙarema Iffah kallo a kaikaice cike da mamakin ƙarfin halin yarinyar, dan tunda yake a wannan masarauta bayan shi babu wani mahaluki daya taɓa zuwa wannan wajen sai Shahan-shan da hadiman dake kula da wajen. Amma a yau sai ga yarinya ƙarama da babu alamar tsoro a cikin idanunta a wajen. Sai kuma yanda tayi kamar bata gansa ba yay matuƙar ƙona masa rai amma ya dake dan yana buƙatar ganin ƙarshen wasan….

Wajen duk da filine na karshen ginin (rufinsa kenan) ya ƙawatu da abubuwa kashi-kashi na more rayuwa. Ga wani ƙamashin furanni da aka ƙawata waje dana fresh air masu narkar da jinin mutum da sanya kasala. Da sauri ɗaya daga cikin hadiman da suka shigo wajen da abubuwa a hanunsu ya ƙarasa ga Tajwar Eshaan dake murza goshinsa kansa a ɗan rissine ƙasa. A gabansa ya dirƙushe yana mai miƙa masa kufan takobin hanunsa da babu tantama anyi adon jikinsa da gold ne. Takobin ya ɗaura masa kan dogon trayn da kufan yake. Hadimin ya miƙe da sauri yana ja da baya. Na biyu ya iso da sauri shima, sai dai saɓanin na farko shi bayansa ya koma yana warware farar rigar hanunsa mai maɗauri. Hannayensa ya ware da ɗan kai idanunsa inda Iffah ke tsaye tana tsiyaya shayi a karamin kofi, ya wani irin ɗage kafaɗu da juya rigar cike da salo ta rufe jikinsa tare da zarge igiyoyin biyu akan damammen cikinsa. Hadimi na uku ya iso shima ya durƙushe hanunsa dauke da ƙaramin farin towel. Nan ma dai ɗauka yay ya rataya a kafaɗa bayan ya ɗan tsane zufan daya taru masa a gefen wuya da goshi alamar dai jininsa a tsinke yake a lokacin.

A yanda hadiman suka sani daga haka hanyar da zata maidashi bedroom ɗin daya kwana yake bi, acan zai samu shayinsa na ƙa’ida mai dafawa ta kai, bayan yasha zai shiga wanka kafin ya fito inda aka shirya masa karin kummalo. Sai dai saɓanin yau yana ɗaga ƙafa domin barin wajen bayan ya dubi Aamin nasa ya rissinar da kai kaɗan na alamar sallama da girmamawa a garesa Iffah dake faman baza ƙamshin da ga Shahan-shan ɗin kawai suka sansa ta isowa wajen ɗauke da ƙaramin kofin shayi dake tururi fari tar na glass.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button